A zauren majalisar dokoki Gobara a farfajiyar majalisar dattawa, yan majalisa sun tsere da gudu

A wani dakin aikin dake ginin ya kama da wuta a safiyar ranar alhamis 15 ga wata yayin da dattawan ke kai-kawo a zauren

  • Published:
Fire accident at National Assembly sends Senators on the run play

Bukola Saraki

(Nigerian Senate )
24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Gobara ta kama a wani sashe na farfajiyar majalisar dattawa wanda ya sanya wasu yan majalisar tserewa domin kubita daga inda wuta ke ci.

A wani dakin aikin dake ginin ya kama da wuta a safiyar ranar alhamis 15 ga wata yayin da dattawan ke kai-kawo a zauren su.

Gobarar ta faru ne sanadiyar lalacewar na'urar bada iska dake daidai dakin kula da ayyuka na bangaren majalisar dattawa  na zauren yan majalisun Nijeriya.

Ma'aikata da baki sun tsere don neman tsira har zuwa ga lokacin da jami'an zauren suka samu damar kashe gobarar.

Jim kadan bayan faruwar haka, dan majalisa Abdullahi Gobir yayi koken cewa zauren bata kai ga zaman inda yan majalisa zasu zauna.

Sakamakon gobarar da ya faru shugaban majalisar Bukola Saraki ya daga ranar zaman yan majalisar zuwa ranar talata 20 ga wata 2018 inda za'a daura daga inda aka tsaya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.