ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

kalaman Buhari ya tada kura, fadar sa tace anyi ma kalaman mummunar fahimta

kan wannan batun wanda ya zama abun muhawara a fadin Nijeriya, fadar shugaban ta mayar da martani

A wajen taro ta musamman kan kasuwanci na kasashe rainon Ingila wadda aka gudanar a birnin Londan shugaban ya furtar da wannan kalaman.

Sai dai wannan kalaman tasa ya tayar da kura a kasar Nijeriya inda matasa suka nuna damuwarsu tare da leka wa furucin a matsayin cin fuska gare su.

Matasan har yanzu suna cece-kuce kan kalaman a kafafen sada zumunta tare da mayar ma shugaban martani na nuna irin kokari da bajinta da matasan nijeriya ke nunawa wajen gudanar da rayuwar su na yau da kullum.

Martanin mukarraban shugaban kasa

ADVERTISEMENT

Kan wannan batun wanda ya tayar da kura kuma ya zama abun muhawara a fadin Nijeriya, mukarraban shugaban sun mayar da martani.

Hirar shi da gidan telebijin na Channels, kakakin shugaban, Femi Adeshina yace yan Nijeriya sunyi ma shugaban mummunar fahimta domin ba duka matasan ya hada wajen yi masu kudin goro ba.

A cewar sa wasu makiyan shugaban suka yi amfani da wannan damar wajen ruruta furucin sa wanda suka yi ma fahimtar iska domin watsa ma shugaban kasa a ido.

Haka zalika shima mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai, Sha'aban Sharada ya kara da cewa matasan basu fahimci kalaman shugaba Buhari.

Yace "Duk wanda ya kalli bidiyon Shugaba Muhammadu Buhari zai ga cewa ya furta kalaman ne cikin raha".

ADVERTISEMENT

Ya ce furucin da shugaba Buhari ya yi hannunka mai sanda ne ga al'ummar kasar domin su tashi tsaye wajen neman na kansu.

Ya kara da cewa a ko wanne lokaci batun yadda za a inganta rayuwar matasa shi ne babban abun da Shugaba Buhari ya sa a gaba.

Sai dai har yanzu dai batun yana cigaba da kumari a yanar gizo, wasu na ganin cewa matasan suka taimaka matuka wajen sa shugaban a kujerar da yake yanzu don haka sun bukace shi da ya nemi gafarar su.

Wasunsu kuma na da ra'ayin cewa gaskiya ce zalla shugaban ya fada, don haka babu wani abin tada jijiyar wuya.

Kalli bidiyo inda ya furtar da kalaman da ya zama abun muhawara a kasar Nijeriya nan kasa

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT