ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kungiyar malamai ta NUT zata gudanar da yajin aiki bisa korar da gwamnati tayi

Kungiyar tace matakin ya zama dole ganin yadda gwamnatin jihar ke ta baiwa malaman takardar sallama

Wannan labarin ya fito bisa sanarwan da mataimakin sakataren kungiyar Adamu Anglo ya sanya hannu kuma ya fitar ranar 4 ga wata wanda yan jarida suka samu a ranar lahadi.

Wannan sanarwa ta zagaye dukanin kananan hukumomi 23 dake jihar bayan kungiyar ta baiwa gwamnatin jihar damar kawar da wannan matakin da kuniyra zata dauka.

Kungiyar tace matakin ya zama dole ganin yadda gwamnatin jihar ke ta baiwa malaman takardar sallama yayin da aka dawo aiki bayan hutun kirismeti da sabin shekara.

ADVERTISEMENT

Wa'adin da kungiyar ta fitar ya kara haske akan wasu batuwa da gwamnatin jihar ke neman katse wa malamai irn su, sanya malaman makarantar sakandare yin murabus kafin sukai ainihin shekarun daina aiki wanda doka ta kafa

Wani batu da kungiyar ke neman gwamnati da biya shine biyan kudin sufuri ga malaman firamare 3,338 na shekara 2015, 2016 da 2017 duk da cewa an ciree kudin domin wannnan manufar.

Hakazalika malaman suna neman gwamnatin da ta biya albashin malamai sama da 15,000 na tsakanin watan Yuni na 2015 zuwa Yuli na Yuli.

Daga karshe NUT ta jaddada cewa gwamnati bata cinma burin malamai ba domin da yaewa ciki su ba'a biya albashin su haka kuma wasu da dama basu samun albashin da ya kamata.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari kungiyar tace gwamnatin jihar ta kasa bunkasa harkar ilimi a jihar ta hanyar tallafawa da malamai da kayan aiki da kuma ingantaccen na'urorin aikin koyarwa da sauran su.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT