ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kubitar da yara 7 tare da kama wasu matasa 3 masu garkuwa da yara kanana a garin Kano

Yayin da suka kama masu garkuwan, jami'an sun samu damar kubitar da yara bakwai daga maboyar da suka aje su.

Rundunar yan sanda dake jihar Kano ta kama wasu gawurtaccen masu garkuwa da yara a garin Kano kana sun kubitar da yara 7.

Bisa ga rahoton da muka samu wannan lamarin ya faru ne ranar alhamis 16 ga watan Nuwamba a garin Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda DSP Magaji Musa Majia ya tabbatar da kamun masu laifin masu suna kamar haka: Khalifa Usman wanda aka yi wa lakanin Gurgun Layin Pole na kurna da  Idris Aminu daga Lokon Sheshe Quarters Kano da  Abdullahi Aminu wanda aka fi sani da Sharu na Sharifai Quarters.

Dsp Magaji yace hanyar da suke amfani dashi wajen tafiyar da barnar da suke shine, idan sun kama yara daga birni sai su tafi dasu kauyukan wasu kananan hukumomin kamar Dambata da Gwarzo Da Gezawa inda zasu mika su ga mai unguwar kauyen a matsayin yaran da suka tsinta a hanya kana su bukaci iyayen yaran da su tura masu katin waya kafin su samu yaran su.

ADVERTISEMENT

Labari ya nuna cewa sun samu katin waya wanda ya wuce N100,000 daga iyayen yara.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT