ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

“Abun takaici ne ganin cewa soja na aikin yan sanda” inji kakakin majalisa

Dogara yace tura sojoji zuwa jihohi 28 a kasar da aka yi yana nuna cewa dokar kasar ya baci

Speaker of the House of Representatives, Yakubu Dogara

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya nuna bacin rai sa game da wasu ayyuka da jami’an sojoji ke yi wanda a kundin tsarin mulkin kasa ayyukan yan sanda ne.

Ranar litinin 3 ga watan Yuli, kakakin ya bayyana cewa tura sojoji zuwa jihohi 28 a kasar yana nuna cewa dokar kasar ta baci.

Ya bayyana haka a garin Abuja a wani shiri na taron tattaunawar ganin kimar kwamitin tsaro a majalisar wakilai.

Hukumar tafiyar da alamuran siyasa da bada shawarwarin doka ta gabatar da shirin.

ADVERTISEMENT

Dogara ya bayyana cewa sashe 217 na kundin tsarin mulki na 1999, ya yi bayanin ayyukan da sojoji zasu yi ba kamar yanda suke a halin yanzu.

Akan batun rashin tsaro da ake fama dashi a kasar, kakakin yace a shirye majalisa take don taimaka wa gwamnatin tarayya wajen bada dokoki na tabbatar da tsaro.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT