ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan majalisa zai yi kwanaki 38 a gidan kaso bayan kotu taki bayar da belin sa

An gurfanar dashi gaban kotu ne kan laifuffaka da suka hada da safarar makamai da garkuwa da mutune

Sanatan ya ziyarci kotun majistare dake nan jihar Kogi a cikin makarar asibiti domin sauraron hukunci da za'a kafa kan laifin da ake zargin sa dashi.

An gurfanar dashi gaban kotu ne kan laifuffaka da suka hada da safarar makamai da garkuwa da mutune.

A zaman kotu da aka yi ranar laraba 2 ga watan mayu kotu ta bashi damar yin beli akan naira miliyan 90, sai dai daga bisani bayan fitowar sa daga kotun yan sanda suka sake kama shi inda suka shigar da laifuffuka da suke zargin sa dashi.

A zaman kotu da aka yi a daidai karfe 9:17 na safiyar ranar alhamis, alkalin sa, Mike Ozokome ya bukaci kotu da ta ba wanda yak wakilta damar yin beli, sai dai wakilin jami'an tsaro ya nemi kotu da ta bada damar cigaba da tsaran dan majalisar har sai an tabbatar da ranar sauraron hukunci sa.

ADVERTISEMENT

Babban alkalin kotun Sulaiman Abdullahi, ya bada umarni na a cigaba da tsaran dan majalisa a gidan kaso har ranar 11 ga watan Yuni inda za'a cigaba da sauraron karar da aka shigar a kansa.

Shi dai Dino Melaye yana cigaba da fuskantar matsi daga jami'an tsaro bisa shaidar da wasu yan tawaye suka bayar na cewa shike ke daukar nauyin abubuwan da suke yi.

Kan wannan rundunar yan sanda ta tura masa tsammaci na ya ziyarci ofishin su domin wanke kansa kan zargin da ake masa.

Sai dai sanatan yaki amincewa da gayatar da yan sanda suka mashi wanda dalilimn hakan rundunar ta sanar dashi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT