ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan majalisa da aka kama, ya fita daga hannun jami'an tsaro

Ma'aikatar shige da fice ta sanar cewa jami'an ta sun kama dan majalisar bisa umarni da aka basu

Sanatan ya sanar a shafin sa na kafar sada zumunta cewa jami'an sun kama shine ne hanyar shi na zuwa kasar Morocco inda zai gabatar da aiki wanda gwamnatin tarayya ta tura shi yi.

Jim kadan bayan kama shi hukumar shige da fice ta sanar da dalilin kama dan majalisar.

Mai magana da yawun hukumar Sunday James ya sanar cewa jami'an NIS sun kama shi ne bisa umarni da aka basu na yin haka.

Sai dai kakakin sanatan, ya shaida ma jama'a cewa mai gidan sa ya fito daga hanun wadanda ke tsaran shi.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa rundunar yan sanda ta musanta sa hannu wajen kama shi, kakakin sa ya sanar cewa "An sake shi kusan sa'a daya da ya shude.

"An sake shi ne bayan yan sanda basu samu abun aibi  a tare dashi. Jami'an NIS da suka taimaka wajen kama shi daga baya sun ji kunyar abun da ya faru ganin yadda yan sanda suka gaza garkame shi"  ya kara.

Sai dai wannan lamarin da ya faru a safiyar ranar litinin 23 ga wata, ya biyo bayan makkonnin da dama bayan rundunar yan sanda sun kaddamar da shi a matsayin wanda suke nema bisa zargin daukar nauyin wasu yan tawaye da suka kama.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT