ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dalilin da yasa shugaba ya makale a Londan bayan ya bar Amurka

Shugaban ya bar kasar ne bayan ya gana da shugaba Donald Trump inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwa na raya kasa

Shugaban ya bar kasar ne bayan ziyarar da ya kai kasar inda ya gana da shugaba Donald Trump inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwa na raya kasa.

Sai dai bayan ganawar tasu shugaban ya bar birnin washington zuwa gida Nijeriya, sai dai dawowar shi ke da wuya, ba'a gan isowar sa.

Wannan lamarin ya janyo tsegumi tsakanin yan Nijeriya inda mafi yawanci ana neman sanin inda ya makale.

Dalilin da yasa ya yada zangon birnin London

ADVERTISEMENT

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu, yayin karin haske game da dalilin da ya sa shugaban bai dawo ba a ranar da ake tsammani.

Ya shaida wan manema labarai cewa, shugaban yayi tafiya ne da karamin jirgi kasancewa ana gyaran babbar jirgin da ya saba tafiya dashi.

Kamar yadda ya sanar, karamin jirgin yana da iyakar nisan zango da zai iya tafiya don haka jirgin ya tsaya birnin London domin a kara mai tare da duba lafiyar ta.

Sai wannan yada zangon da shugaban yayi zuwa London ya janyo cece-kuce ga yan kasa musamman ma daga yan jam'iyar adawa ta PDP.

PDP a cikin wata takarda da ta tura ma manema labarai, tana zargin shugaban da sabawa doka bisa tafiyar da yayi ba tare da ya sanar ma majalisar dokoki.

ADVERTISEMENT

Ta kara da cewa yan Nijeriya na da hakkin sanin dalilin da yasa ya tafi London da kuma adadin kudin kasa da ya kashe sakamakon tafiyar tasa.

Shugaban dai ya dawo kasar a daren ranar alhamis 3 ga watan Mayu a mai makon ranar laraba da ake tsammani.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT