ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari zai sa hannu ga doka na baiwa matasa damar tsayawa takara

Kudirin dai zai baiwa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Domin raya ranar dimokradiya, shugaban ya bayyana hakan ne a wajen jawabin sa safiyar ranar talata.

Tun a cikin watan yuli na 2017 majalisar tarayya ta amince da kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa da jiha da sauran kujerun siyasa na kasa.

Shugaban yana mai cewa "Nan da 'yan kwanaki kadan zan sadu da matasa da dama na kasar nan domin sanya hannu kan kudurin dokar da za ta bai wa matasa damar tsayawa takara."

Haka zalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT