ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ana cikin yarjejeniyar kan sakin yan kasa da Boko haram ta sata

Shugaban yayi kira ga jami'an tsaro da su zage damtse wajen tabbatar da tsaro a makarantu dake fadin kasar.

Shugaban yana mai cewa gwamnatin sa zata iya bakin kokarin ta wajen kubitar da duk wanda yan ta'adar suka garkame.

Mai baiewa shugaban shawara musamman a kan watsa labaraiFemi Adeshina ya bayyanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar litinin 26 ga wata.

A cewar shi shugaban ya dauki wannan alkawarin yayin da ya amshi bakoncin malamai da matan da yan ta'adar suka saki kwanan baya.

ADVERTISEMENT

Shugaban yace gwamnatin sa na kokartawa wajen kubitar a wasu yan kasa da mayakan boko haram suka sace kuma a halin yanzu shine batu mafi muhimmanci a gare su. Shugaban yace ana la'akari da lafiyar su wajen tabbatar da sun dawo ga iyalen su cikin koshin lafiya.

Daya daga cikin malamai da aka kubitar Dakta Solomon Yusuf ya jinjina ma gwamnatin bisa kokarin data yi wajen ganin sun dawo ga iyalen su.

Adeshina yace shugaba Buhari ya sanar da malamai da matan da aka sace cewa hanyoyi da aka bi domin ganin sun kubita daga hannun  yan ta'adar ya wahalar dasu kasancewar yan ta'adar sun bazu a wurare da dama.

Shugaban ya umarci jami'an tsaro da su zage damtse wajen tabbatar da tsaro a makarantu har ga dalibai dake fadin kasar.

Shugaban ya nuna bakin cikin sa bisa harin da yan ta'adar suka kai makarantar  Government Girls Science and Technical College dake nan garin Dapchi na jihar Yobe.

ADVERTISEMENT

Har yau dai ana kai kawo wajen gano hanyar kubitar da wadannan dalibai.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT