ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar shelkwatar EFCC wanda aka gina da naira biliyan 24

Sabuwar ofishin zai kasance ainihin cibiyar hukumar na din-din-din bayan ta kwashi shekaru da dama tana zaman haya.

An gina sabuwar hedkwatar EFCC da naira biliyan ashirin da hudu (N24BN).

A jawabin sa wajen kaddamar da cibiyar, shugaban yace matakin da gwamnatin sa ta dauka wajen yakar cin hanci da rashawa mataki ne na kubutar da kasar ba don tuhumar wasu tsararrun mutune ba don wata manufa daban.

Tun a cikin shekarar 2010 gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta amince da gina ofishin mai benen hawa goma.

Tuni dai wasu ke cece-kuce game da kudin da aka kashe kan gina sabuwar ofishin.

ADVERTISEMENT

Shugaban hukumar, Ibrahim ya sha suka bisa kashe N24bn sabanin ainihin naira biliyan 18 wanda aka kayyade tun asali. An kammala ginin ne bisa canji da aka samu na darajar kudin Nijeriya.

Yayin da ya zanta da gidan telebijin na Channels, Magu yayi karin haske game da kudin da aka kashe wajen gina ofishin. A cewar shi, ya bar al'amarin ga jama'a domin suma su zo su gan ginin kana su bada shaidar yanayin aikin da suka gani da yanayin tsare-tsare da aka yi.

Sabuwar cibiyar zata kasance tamkar ta cibiyar FBI ta kasar Amurka.

A makon da ya gabata, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki tare da takwaran sa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun ziyarci sabuwar ofishin.

Sun yaba ma hukumar EFCC bisa aikin da aka yi wajen gina cibiyar tare da bada tabbacin cigaba da goyon bayan hukumar wajen kawo karshen cin hanci da rashawa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT