ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Buhari ya gana da iyayen yan matan makaranta da aka sace a dapchi

Ya tabbatar masu cewa gwamnatin sa baza ta huta ba har sai bayan yaran sun dawo gare su

Ganawar shi da iyayen makarantar gwamnati ta kimiya da fasaha dake Dapchi inda aka sace yaran, shugaban ya jajanta ma iyayen tare da sanar masu cewa Allah zai cigaba da kwantar da hankalin su yayin da gwamnatin sa ke kokartawa wajen kubutar da yaran da aka sace.

Ya tabbatar masu cewa gwamnatin sa baza ta huta ba har sai bayan yaran sun dawo gare su bisa matakin da gwamnatin sa ta dauka na sasanta da mayakan boko haram wajen kubutar da yaran.

A wata takardar da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar, shugaban yana main cewa "Na karatan rahoton da aka kawo mun kan abun da ya faru a Dapchi. Sanda ya samu rahoton ina mai cike da bakin ciki kuma ina taya ku da addua'r Allah ya baku hakurin juriya".

Shugaban yayi karin haske kan matakin da gwamnatin sa jke dauka wajen yaki da ta'adanci inda ya sanar ma iyayen cewa sojoji zasu fatattaki mayakan.

ADVERTISEMENT

Yace zasu iya bakin kokarin su wajen ganin an kawo karshen ta'adancin boko haram kuma ya umarci jami'o'in tsaro da su cigaba da bincikle har sai yaran siun dawo ga iyayen su cikin koshin lafiya.

Bashir Manzo  ya wakilci sauran iyayen a yayi kira ga gwamnati da tayi iya bakin kokarinta wajen kubutar da yan matan.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT