ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

'Na kusa dawowa domin jagorar najeriya' Shugaba ya gaya wa Gwamna Bello

Buhari ya faɗa wa Bello cewa ya ji lafiya, bisa bayanin da kakakin Gwamnan, Kingsley Fanwo ya faɗa.

President Buhari (L) and Gov Yahaya Bello of Kogi (R)

Buhari ya faɗawa Bello cewa ya ji lafiya kuma “lafiyar shi lau” , bisa bayanin da kakakin Jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya faɗa.

Fanwo ya faɗa cewa Buhari da Bello sun yi magana a kan waya, a lokacin da gwamnan ke kan hanyar dawowa daga Garin Abeokuta a Jihar Ogun, inda ya je bikin ranar haihuwar tsohon Shugaban ƙasar najeriya, Olusegun Obasanjo, na cika shekara 80.

Kakakin Bello ya ƙara cewa wai, hiran ya faru a gaban ɗan majalisar dokokin Jihar Kogi, Ahmed Imam, tare da wasu manyan ƴan jihar Kogi, waɗɗanda suka raka shi zuwa Abeokuta.

“Shi Shugaba (Muhammadu Buhari) ya gaya wa gwamna cewa yana hutawa, kuma ya kusa dawowa Nijeriya domin cigaba da aikin sa na samad da shugabanci mai kyau ga al’umma” Fanwo ya ce.

ADVERTISEMENT

Buhari ya yi magana da Obansanjo, tare da taya shi murna, akan bikin ranar haihuwar shi.

A cewar kakakin Buhari, Femi Adesina, Shugaba ya bayana Obasanjo a matsayin gaskiyar ɗan kasar duniya. Adesina ya ƙara cewa Obasanjo ya yi wa Buhari Addu’a ƙarin lafiya mai kyau, da cewa “yana tsaye da shi a Addu’a”, domin ya dawo da sauri ya cigaba da kyakkawan aikin da yake yi a ƙasar.”

Obasanjo a lokacin bikin ranar haihuwar sa ya ce, buhari na da ƙarfi a al'amurran gwagwarmaya da makami da kuma cin hanci da rashawa, amman ba shi da ƙarfi a ɓangaren tattalin arziki, da kuma harkokin ƙasar waje.

Shugaba Buhari ya je london tun 19 na janairu, a lokacin da ya bar Nigeria domin abin da ya kamata ya zama kwana 10 na hutu.

Amma shugaba ya rubuta wasiƙa zuwa ga majalisar dattawa, da cewa su tsawaita masa hutun, bayan bayyana cewa ba zai iya barin London ba sai likitocin shi sun soke “wasu Dalilai”

ADVERTISEMENT

Amman ƴan hukuma daban daban, haɗe da mataimakin shugaba Yemi Osibanjo tare da shugaban yan majalisar dattawa, Bukola Saraki sun ce lafiyar Shugaba kalau.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT