ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan ta’ada sun shirya mika wuya ga hukumar kare lafiyar jama’a a jihar Borno

Shugaban hukumar na jihar Borno Ibrahim Abdullahi ya bayyana haka a wata hira ta musamman dayayi da kamfannin dilancin labarai (NAN) ranar laraba a garin Maiduguri

Hukumar kare lafiyar jama’a reshin jihar Borno tace mutum 40 daga cikin ƙungiyar yan tawaye na Boko haram sun shirya mika wuya gare su.

shugaban hukumar na jihar Borno Ibrahim Abdullahi ya bayyana haka a wata hira ta musamman dayayi da kamfannin dilancin labarai (NAN) ranar laraba a garin Maiduguri

Abdullahi ya sanar cewa yan tawayen sun bayyana anniyar su ga wani majiyin su a cikin sirri kuma har yanzu suna yarjejeniya cikin labule game da mika wuyan su.

Kwamandan ya bayyana cewa mutum 6 shida sun mika wuya ga hukumar shi kuma sun yi haka da son ran su karkashin tsarin kariya na ‘safe corridor initiative’ da gwamnatin taraya ta kirkiro domin kiran yan tawaye dake neman mika wuya.

ADVERTISEMENT

NAN sun ruwaito cewa daruruwan yan tawaye suka mika wuya ga rundunar sojoji karkashi wannan tsarin da ake kirkiro.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT