Boko Haram ʼƳan Mata masu kísan kai sun kai hári a garin Kamaru, mutane huɗu sun ji rauni

ʼƳan Mata guda biyu sun shiga garin babu takalma da sáfe, a ránar kasuwan Talata.

  • Published:
ʼƳan Mata masu kísan kai sun kai hári a garin Kamaru, mutane huɗu sun ji rauni play

ʼƳan Mata masu kísan kai sun kai hári a garin Kamaru, mutane huɗu sun ji rauni

24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Ana zargi cewa wásu ʼƴan matan Boko Haram biyu, sún kái hári a cikin wani garin da yáke iyakár Kamaru da Najeriya. Wannan ya faru a ránar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2016. ʼƳan jaridan Reuters suka kawo wannan rahoto.

Shugaban ƙaramin hukumar Mayo-Sava, mai suna Babila Akaou, ya yi bayáni cewa nakiya na farko ya tashi a Mora. Ɗaya daga cikin ʼƴan matan ta mutu a nán táke, kuma mutane huɗu sun ji rauni.

ʼƳan unguwa sun kashe ʼƴar uwanta kafin nakiyan da yake ɗaure da ita ya tashi. ʼƳan ɗarikar Boko Haram sun sha yin amfani da ʼƴan mata da yara wajen ta da nakiyoyi kai-akai. Waɗanan ʼƴan mata suna da shekara tsakanin 13 da 18. ʼƳan tsaró sun gani lokacin da suka shiga garin Akaou da safe a ranar kasuwa. Wani ɗan gari mai suna Abou ya ce:

"Sun kama hanyar kasuwa. Ba su sanyá takalmá ba, wannan shi yá jáwo hankalin mu zuwa wajen su."

Abou yá ce ʼƴan matan sun wuce gaban shi a daidai ƙarfe bakwai na safe.

Masu kisan kai suna kai hari a Mora wanda yake kilomita talatin daga iyakan Najeriya. Sun kai irin wannan hari cikin Kamerun kullum, amma ƙungiyar International Crisis Group sun yi rahoto a wannan wata cewa an rage hári sosai tun watan Satumba. Wannan ya sa manazarta su yi imani cewa  ƴan Boko Haram sun rasa ƙarfi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.