ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kara samun dabba mai hadiye makudan kudi

Sanata Shehu Sani yace biri ya hadiye kudin da aka ware ma yan majalisar dattawa a gonar Sanata Abdullahi Adamu

A bisa labarin dan majalisar, birai suka yi gaba da naira miliyan 70 mallakin gammayar yan majalisar daga arewacin kasar a gidan gonar tsohon jagoran gamayyar.

Bayan wata wasikar da kakakin kungiyar Dino Melaye yayi inda aka nemi a sauke shi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban su bisa wasu zargi da ake mashi wanda ya hada da yin badakala kudin kungiyar.

Sanata Shehu Sani yana mai cewa; "Akwai wasu abubuwa da abokanan aikina basu fada ba amma ni yau ba zan yi shuru ba. sanda muka shiga zauren nan, sanata Ahmed Lawan ya kaddamar da N70 ga wannan zauren tamu na kudin da aka samu da yan majalisar da suka gabata kafin shigowar mu. Nan take aka mika kudin ga kungiyar sanatocin arewa.

Jita-jita yana ta yaduwa wanda bani da tabbacin ta amma na san wasu daga cikin yan majalisa suna sane cewa ana zargin cewa birai sun far ma gidan gonar daya daga cikin jagororin kungiyar har ma suka samu damar kubita da kudin.

ADVERTISEMENT

"Ina ganin lamarin wannan kasar ya fra komawa abun dariya. Da farko beraye suka kori shugaban kasa daga ofishin sa kana mun samu labarin maciji mai hadiye nair miliyan N36 yanzu kuma mun samu birai masu sata a gidan gona. Ba so jin haka ba amma ina tunanin yanzu kowa ya san gaskiyar lamarin.

Game da cire Abdullahi Adamu daga matsayin shi, Dino Melaye yace matakin ya fito ne bayan amincewa daga mafi yawancin yan majalisar dake zauren.

Wannan shine karo na biyu da muke jin cewa dabba ta hadiye makudan kudaden jama'a.

Kwanakin baya mun ruwaito cewa wata ma'aikaciyar hukumar dake shirya jarabawar shiga jami'a ato JAMB mai suna Philomina Chieshe ta zargi cewa maciji ya hadiye miliyan N36 na kudin hukumar a ofishin ta .

A cewar ta mai aikin gidan ta tare da abokiyar aikin ta Joan Asem suka hada hannun wajen wawushe kudin ta hanyar tsubbu daga asusun ajiya na hukumar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT