ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Abubuwa 10 da muka gano daga cikin jawabin shugaban ƙasa

Ba da dadewa shugaba Buhari yayi ma ƙasar jawabi yayin da ake murnar cika shekara 57 da samun yanci daga mulkin mallakar turawah. Ga abubuwa da muka gano daga cikin jawabin

A Jawabin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi a yau yayin da ake murnar cika shekaru 57 da samun yancin kai yayi magana ne akan tsaro, yakin neman sauya fasalin ƙasa, cin hanci da yadda za’a bunkasa harkan kasuwanci a ƙasar.

Ga abubuwa 10 da muka fahimta daga cikin jawabin sa kamar haka;

1. Buhari ya daura alhakin fitowar ƙungiyar IPOB ga shugabannin kudancin ƙasa

Shugaban ƙasa ya jaddada cewa ƙasar baza ta rabu karkashin mulkin shi.

ADVERTISEMENT

Yayin da ƙungiyar dake faffutikar kafa ƙasar biyafara IPOB wanda Nnamdi Kanu ke jagoranta ke neman haifar da riƙici a yankin kudancin ƙasar, Buhari yayi ma shugabannin siyasa da ma na gargajiya kira inda yake cewa;

“Ina bakin ciki ganin cewa shugabannin al’ummar yankin basu yi ma matasan su gargadi ba akan abubuwan da ya faru a yakin ƙasa na shekaru baya. Wadanda suka gan abubuwan da ya faru su bayyana ma wadanda basu gani ba yadda alamarin ya kasance.”

2. Masu faffutikar neman raba kasa basu san ciwon kansu ba

Buhari yace kiranye da ake domin sauya fasalin ƙasar har yanzu ana yi kamar yadda ya kamata.

Yana kokawa cewa sanadiyar hakan ya haifar da wasu ƙungiyoyi masu son a raba ƙasar ta hanyar riƙici.

ADVERTISEMENT

3. Buhari yace masu neman a canja fasalin ƙasa su bi hanyar da doka ta tsara

Duk da kuran da ake tadawa a yankin kudancin ƙasar har ma da yankin Nija delta don ganin an raba ƙasar, shugaban ya jaddada cewa dole sai magoya bayan hakan ya faru sunbi yadda doka ya umarta ba ta hanyar riƙici ba.

4. Shugabannin baya basu tanaji komai ma ƙasar

A bisa bayanin shugaban shugabannin kasar na da basu tanji komai ma kasar domin sunyi amare da kudaden da aka samu ta hanyar mai shiyasa ya gaji mulkin wadda ke cikin halin tangalda a fannin kasuwanci.

5. Babban abokin gaba na ƙasar shine cin hanci da rashawa

ADVERTISEMENT

Shugaban ya ci zaben shugaban kasa domin mutane da dama suna ganin yayyi kaurin suna indai fannin yaki da rashawa ne.

A jawabin sa ya ayyana cewa har yanzu ya tsaya a kan bakan yakar wannan halin dake neman cinye kasar kuma zai zage damtse wajen ganin an samu nasara.

6. Buhari yace idan kun mai aikata abun da bai kamata ba ku kai kara

Shugaban yace yaki da rashawa da gwamnatin sa keyi zata samu nasara idan yan ƙasar taimaka wajen tabbatar da hakan.

ADVERTISEMENT

7. Ku cigaba da nuna farin cikin ku a ko wani ranar 1 ga Octoba na ko wani shekara

Kasancewa ƙasar ta samu kalubale da dama tunda ta samu yancin kai a 1960, shugaban yana son ko wani ƙasar ya nuna farin cikin sa duk lokacin da wannan ranar ta zagayo.

8. Za’a sauya tsarin mahukunta domin yaki da rashawa

Masu sharhi sun bada shawara cewa indai an gyara yadda tsarin shari’a take a ƙasar shine za’a samu nasarar yakar cin hanci da rashawa.

Shine shugaban ya yarda da haka domin yace a karkashin mulkin shi za’a canja tsarin mahukunta na ƙasar domin tabbatar cewa an kawar da cin hanci a ƙasar.

ADVERTISEMENT

9. An samu gyara a fannin wuta

Banda alkawarin da ya dauka na cewa gwamnatin shi zata gaggauta ayyuka cikin nan da shekara 2, shugaban ya kara da cewa fannin wuta na kasa tana samun gyara kamar yadda ya kamata.

10. Buhari yayi alƙawarin bunkasa ƙasa cikin nan da shekara biyu

Sama da shekara biyu kenan da shugaban ya hau kujerar mulkin ƙasa kuma saura kusan shekara biyu da mulkin shi zata kare.

Shugaban yayi alƙawari cewa ‘yan Nijeriya zasu gan gyara kafin 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Here are common things people rarely dream about

Here are common things people rarely dream about

5 young women who embody Y2K and alte fashion

5 young women who embody Y2K and alte fashion

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT