ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya ta bada hutun kwana biyu

Ministan ayyuka na cikin gida ya sanar da haka a garin Abuja ranar litinin

Eid-el-kabir

Gwamnatin tarayya ta bada ranar juma’a 1 ga watan satumba da litinin 4 ga watn satumba a matsayin ranar hutu don ma’aikata suyi murnar bikin Eid-el-kabir.

Ministan ayyukan cikin gida LT.Gen Abdurahman Dambazau (mai ritaya) yayi wannan sanarwan a madadin gwamnatin tarayya a garin Abuja ranar litinin 28 ga watan agusta.

Ministan yayi kira ga musulmai da ma sauran yan Nigeria da su yi amfani da wannan damar suyi ma kasar addua na samun zaman lafiya, hadin da samun nasara.

Dambazau ya roki yan NIgeria da hada kai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen neman zaman lafiya da hadin kai.

ADVERTISEMENT

Ya tabbatar cewa duk wani mataki na neman tsaro gwamnatin ta riga ta tsara shi kuma dukanin jami’an tsaro a shirye suke wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin da ake bikin babban sallah har zuwa bayan bikin.

A karshe ministan yayi ma yan Nigeria fatan alheri.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT