ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan majalisar dattawa yana jinjina wa kungiyar kwadago da na malamai game da zanga-zanga da suke yi

Kwannan baya kungiyar kwadago da na malamai sun kai fushin su zauren majalisar dokokin na jihar Kaduna ta hanyar zanga-zanga inda har suka yi fashe-fashe a zauren.

Kungiyoyin sun yi hakan ne domin nuna fushin su game da malamai 22,000 da gwamnatin jihar Kaduna ta sallama bisa ga rashin cin nasara a jarabawan yan aji hudu da aka gabatar masu.

Duk zanga-zangar da kungiyoyin keyi gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai yace Babu wata makawa dangane da korar malaman

Sakamakon zanga-zangar da suka ne shine dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin jihar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bayyana ra'ayin sa game da lamarin da ya faru.

Dan majalisan ya rubuta a shafin sa na Facebook:

ADVERTISEMENT

"Ina Jinjina Ma Kungiyan kwadago da Kungiyan Malaman Makarantun Kaduna na tsayawa tsayin daka na Kare yan'cin Malaman Makarantun firamare.Ina Tare da Ku dubu bisa dubu.Koran Malaman Kaduna Bashi da faida.Duk wayanda aka kore su aiki Insha Allahu Lokaci zai zo da zasu Koma.Ku cigaba da gwagwarmaya."

Maganar sa ya janyo tsegumi a kafar sadarwa ta facebook inda wasu ke bada ra'ayin su na cewa inda yaran shi na zuwa makarantar gwamnati ba zai yi irin wannan maganar ba.

Tun ba yau ba dan majalisar da gwamnan jihar Kaduna suka samu sabani kuma da alama har yanzu basu warware ba.

A baya sanatan ya baiwa shugaba gargadi inda yake cewa Buhari ya kare kanshi daga gubar El-rufai

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT