ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon dan majalisar dattawa mai shekaru 87 ya auri yar shekara 47

Ina gwanin wani ga nawa na wannan mako, ai namiji mai kwazo kadai ke iya aikata haka, kash! bari in rike kalaman baki na tunda ni mai kallo ne

Tsohon dan majalisar dattawa na kasa Sanata Cyrus Nunieh ya auri sabon amaryar shi Rosemary a garin Fatakwalt dake nan jihar Ribas.

Anyi gangarumin bikin auren a babban dakin masaukin baki na Presidential hotel dake nan babban birnin jihar.

Sanata Cyrus Nunieh shine lauya na farko da yan kabilar Ogoni suka samu kuma ya auri Rosemary mai shekaru 47 bisa ga damuwa da zaman kadaici bayan rasuwar matarshi a 1991.

Game da auren shi dattijon yace "kasancewa duk yara na sun girma kuma sun kama gaban su na zama ina rayuwa cikin kadaici tunda matata ta rasu a 1991"

ADVERTISEMENT

"Na auri Rosemary ne domin ina sonta hakazalika ita ma tana so na kuma mun fahimci juna"

Shidai sanatan ya nuna cewa babu ruwan shekaru da soyayya ko tsawon kwanar mutum domin babu wanda ya san ranar mutuwar sa kuma mutum na iya yin aure toh batun shekarunsa bata taso ba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT