ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Babban malamin ABU ya rasu rana daya da zama Farfesa

Babban malamin mai suna Dakta Zakari yusuf Ibrahim, ya shahara ne a fannin ilimin kimiya ta Physics

Babban malamin mai suna Dakta Zakari yusuf Ibrahim, ya shahara ne a fannin ilimin kimiya ta Physics. Yayi kaurin suna a jami'o'in arewa musamman ma a ABU da jami'ar Umaru Musa yar'adua dake katsina.

Kamar yadda majiya suka shaida mana, malamin ya rasu rana daya da tabbatar dashi a matsayin Ferfesa.

Wani dalibin makarantar ya shaida mana cewa, malamin ya fadi ne yayin da yake koyar da darasi wanda sakamakon hakan ake garzaya dashi asibiti wanda daga bisani Allah yayi masa cikawa.

Hazikin malamin kafin rasuwar sa shine shugaban sashen ilimin kimiya na ABU.

ADVERTISEMENT

Yayi karatun digiri dinsa na farko da na biyu a nan ABU a bangaren Physics kana yayi digiri dinsa na uku na PhD a kan fannin Nukiliya.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT