ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa yace hotuna buhunan shinkafa mai dauke da hoton shi ba daga gare shi bane

Tawagar Atiku sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa bai fara kamfe ba kuma yin haka baya cikin tsarin yin kamfe da zasu gabatar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar yace hotunan kamfe wanda aka yi a kan buhunan shinkafa ba daga gare shi ne wasu suka kirkiro ta.

Yan Nijeriya sunyi tsokaci akan hoton wanda yayi yawo a yanar gizo.

Offishin watsa labarai na Atiku ta mayar da martani game da tsokacin da jama’a keyi inda tace hoton karya ne kuma yin haka baya cikin tsarin kamfe da zasu gabatar.

“Mun gan wannan hoton yana yawo a yanar gizo. Karya ne wata kila ma an kirkirota ne. Atiku na da makerar abinci, yana samar ma mutane da dama aiki, mai zai sa yayi haka a kan shinkafa.” @atikuorg ta rubuta a shafin su na twitter.

ADVERTISEMENT

Wannan ba shi bane karo na farko da tawagar tsohon mataimakin shugaban ƙasa zasu karyata wani abu dake da alaka da ubangidan su. Bayan wata labari da aka fitar a baya mai cewa Atiku na taimakon shugaban ƙungiya mai faffutikar kafa ƙasar biyafra (IPOB) Nnamdi Kanu, tawagar sunce zasu kai kara ga kotu.

Duk da cewa bai bayyanar da fitowar shi, muna sa ran cewa Atiku zai yi takarar shugaban ƙasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar APC wanda shima shugaban ƙasa Buhari yake kuma wata kila shima zai fito takara.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT