ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jihar Kano ta kaddamar da ranar Juma'a a matsayin ranar hutu

Ana sa ran cewa, gawar shi zata iso Nijeriya ranar alhamis kana za'ayi jana'zar sa a nan garin Kano da misalin karfe 2:30 na ranar Juma'a.

Wannan labarinya fito ne a wata sanarawa da kwamishnan labarai na jihar, Malam Muhammed Garba, ya fitar wa manema labarai ranar laraba 9 ga watan Mayu.

Kamar ya yadda sanarwa ta bayyanar, gwamnatin ta bada hutun ne domin ma'aikatan jihar sun halarci jana'izar babban malamin addini, Sheikh Isyaka Rabiu  wanda ya rasu ranar talata.

Ana sa ran cewa, gawar shi zata iso Nijeriya ranar alhamis kana za'ayi jana'zar sa a nan garin Kano da misalin karfe 2:30 na ranar Juma'a.

ADVERTISEMENT

Labarin rayuwar sa

Marigayin, fitaccen malamin addini ne kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya kafa kamafanin Isyaka Rabiu and Sons.

Cikin yaran sa akwai Nafiu Isyaka Rabiu da Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, shugaban kamfanin BUA da Nafiu Isyaka Rabiu shugaban kamfanin jirgin sama ta IRS.

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Qur'an".

ADVERTISEMENT

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT