ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari yayi ma al'ummar jihar Zamfara albishir na tsawaita tsaro

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin al'ummomi na jihar a zauren gidan gwamnatin jihar

Ziyarar da ya kai jihar ranar laraba 22 ga watan Maris, shugaban ya jajanta ma jihar kan kisan da barnatar da dukiyoyi da ayyukan ta'adanci ya sabbaba a jihar. Ya kalubalanci jami'an tsaron kan su kyautata dangantakarsu da al'ummar jihar ta yadda za su rika samun muhimman bayanai daga gare su kan ayyukan 'yan ta'adda.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin al'ummomi na jihar a zauren gidan gwamnatin jihar.

Shugaban ya kuma yabawa jami'an tsaro kan nasarar da suka samu wajen kashe kasurgumin dan ta'addan nan da aka fi sani da sunan " Buharin Daji", ya kuma kira na a murkushe mabiyansa wadanda suka yi fice wajen kisan mutane.

Daga karshe shugaba Buhari ya baiwa gwamnatin jihar hakuri kan mayar da kudin da ta kashe wajen gyaran titunan tarraya da tayi.

ADVERTISEMENT

Yace ya umarci ministan muhalli da ayyuka Babatunde Fashola da ya biya jihohin da suka aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya.

A jawabin sa, Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta biya kudin domin samun daman dakile matsalolin tsaro da jihar ke fama da ita.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT