Kociyar ya kwashi tsawon shekaru 22 yana horas da sannanen kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila.
Arsene Wenger, kociyar kungiyar Arsenal yayi murabus
Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar
Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar.
Kamar yadda labarin ya fito a shafin kungiyar ta yanar gizo, Arsene Wenger yana ma kungiyar da dinbim magoya bayan ta dake ko'ina a fadin duniya godiya game da damar da aka bashi na jagorantar tawagar yan wasan ta na tsawon shekaru 22.
Dan kasar faransa mai shekaru 63, shine kociya mafi dadewa a tamaular firimiya na Ingila kuma yayi nasarar horar da Arsenal a wassanni 823.
Yayi murabus ne kafin karewar kwantiragin sa wanda sai cikin kakar badi zai kawo karshe.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng