ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An tura dakarun sojoji neman turawa 4 da yan bindiga suka sace

Yan bindigar sun sace turawan hanyar su zuwa Abuja daga Kafanchan bayan sun kashe yan sanda biyu dake basu kariya

An tura dakaru na musamman daga Abuja domin taimakawa jami'an 'yan sanda gano Turawa hudu da yan bindiga suka sace a jihar Kaduna.

Yan bindigar sun sace su ne a sakamakon harin kwantar bauna da suka kai ma tawagar motar su hanyar su zuwa garin Abuja daga Kafanchan ranar laraba 17 ga watan yau.

Artabon da suka da jami'an dake tsaron turawan tayi sanadiyar kashe jami'an yan sanda biyu dake tare da turawan.

Bayan ruwan alburusai da ya faru ne yan bindigar suka samu rinjaye har suka tsere da turawan.

ADVERTISEMENT

Turawan dai sun hada da yan Amurka biyu da kuma yan kasar Canada biyu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar hakan yayin da ya tattauna da manema labarai.

An sace su a babba titin Kaduna zuwa Abuja a dai dai kusa da garin Jere.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT