ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan sarasuka 50 da suka addabi al'umma sun shiga hannu

Jami'an tsaro sun kama su ne a sassa daban-daban dake fadin garin sakamakon binciken da suke game da tarzomar da wasu bata gari suka tayar kwanan baya.

Jami'an sun kama su ne a sassa daban-daban dake fadin garin sakamakon binciken da suke game da tarzomar da wasu bata gari suka tayar kwanan baya.

A wata sanarwa da ya fita, hadimin gwamnan jihar, mista Samuel Aruwan ya jinjina ma jami'an kana ya sanar cewa da zaran an kammala bincike za'a gurfanar dasu gaban kotu.

Ya bayyana cewa gwaman Nasir El-rufai ya samu labarin kamun da jami'an tsaron suka yi kuma yana mai kira na a tabbatar da shari'a bisa ga laifin da suka aikata.

Tun ba yau ba al'ummar garin Kaduna ke fuskantar barazanar yan sarasuka ko yan shara sai dai aika-aikan da suka yi kwanan nan ya jawo hankali wanda daga bisani gwamnan ya ziyarci al'ummar da lamarin ya faru.

ADVERTISEMENT

Bayan ziyaran da ya kai ya umarci jami'an tsaro da suyi bincike cikin gaggawa domin kawo karshen aikin su.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT