Babban kwamandar hukumar na filin jirgin mista Ambrose Umoru ya sanar da haka yayin da ya bayyanar da masu laifin su biyu ga manema labarai ranar alhamis 1 ga watan Maris.
An cafke wasu masu safarar miyagun kwayoyi a filin jirgin sama na Aminu kano
Yace dai an kama su ne yayin da ake binciken bayan saukar su daga jirgin sama
Yace dai an kama su ne yayin da ake binciken bayan saukar jirgi.
Daya daga cikin masu laifi wanda asali da dan karamar hukumar Indemili South dake jihar Anambra ne ya shiga hannu jami'an hukumar bayan na'urar bincike ta bayyana wasu kwayoyi wadanda ya hadiye wanda ake tsammani cewa ta kai kilo 2.180.
Mai laifin wanda ke sana'ar aski a kasar jamhoriyar Congo ya shigo kasar ne da kwayoyin daga kasar Burundi kuma yana kokarin safarar kwayoyin zuwa jihar Anambra dubun sa ya cika.
Dayan mai laifin mace, yar shekara 32 kuma yar asalin jihar Delta ta shigo da fararen gari wanda ake tunanin cewa garin iblis ne ta shigo dasu ne daga kasar Habasha.
Umaro yace matasan Nijeriya sun tsallake rijiya da kafar dama inda yayi la'akari da illar da kwayoyin zasu haifa idan sun samu nasarar shiga dasu kasar.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng