ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ali artwork yayi fashin baki game da gabar Ali Nuhu da Adam A.Zango, yace duk azalumai ne

Yace duk cikin su babu wanda bai more shi ba wajen harkar shi na yin editin amma sai dai suka maida shi tamkar bawa mai bauta domin basu taba bashi ladar aikin sa kamar yadda ya kamata.

Dan wasan yayi wannan raddi a shafin sa na instagram inda yace duk da sanin su suka kirkiri gabar don kada ace kwana biyu an daina jin duriar su.

Ali artwork wanda banda wasan barkwanci sananne ne a bangaren tace bidiyo kafin a sako ta ga jama'a, yace duk cikin su babu wanda bai more shi ba wajen harkar shi na yin editin amma sai dai suka maida shi tamkar bawa mai bauta domin basu taba bashi ladar aikin sa kamar yadda ya kamata.

Ga maganar shi kamar yadda ya rubuta a shafin sa na Instagram;

"Duk abunda kuka GA sunayi suna sane kuma su suke kirkirar hakan don su motsa jam'iyya kar a ce ai kwana biyu an manta da su to ku sani ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata.

ADVERTISEMENT

In baku manta ba a shekaru baya suntaba shirya irin wannan rikicin nasu mu kazo mukai ta cecekuce a kai Amma daga Karshe mai hakan ta haifar sai suka maidamu bamu san komai ba.

Dan haka kusan duk wanda yasa kansa sai yayi dana sani ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu dan ba wanda a cikinsu zai iya kashe min matsalar dubu 200,000 kowa a cikinsu na zauna da shi ba wanda bai moreniba akan harkata ta editing Amma babu wanda na taba WA aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya bani in kuma da akwai ya fito ya karyatani.

Sai dai kai ta bautar banza sun fiso kullum kai ta basu girma suna zalintarka to ku sani anyi walkiya munga kowa #kyar_nake_kallonku ba ruwa na da rigimar wani ni ma takaina nake in kanayi dani inayi da kai in bakayi dani nima baruwa na dakai.

Ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka GA dama ku shirya ku ta dama ni ko a jikina ko kuma mutum ya bar industry din tuda ba da ita aka haifeshi ba don haka mu zamu ciyar da harkar gaba insha Allah tunda ku kunsa Hassada da muna furci da gwara kan masoyanku kuje kuyi tayi don haka ni na dogara GA Allah shine gatana ba wani MUTUM BA".

Sai dai a halin yanzu jarumai Ali Nuhu da Adam Zango sun daidaita tsakanin su bayan wasu masu da tsaki a masana'antar sun nemi a yi hakan.

ADVERTISEMENT

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT