Aisha Alhassan Mama Taraba ta bada hakuri game tsokacin da tayi

Ta bada hakurin bayan ganawar da tayi da jiga-jigan jam’iyar APC

  • Published:
Mama taraba ta bada hakuri game da tsokacin da tayi play

Mama taraba ta bada hakuri game da tsokacin da tayi

24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Ministan ayyukan mata Aisha Alhasan ta bada hakuri game da kalamun da ta furtar na goyon bayan tsohon mataimakin shugabam ƙasa Atiku Abubakar a zaben 2019.

Wannan ya fito bayan ganawar da tayi da jiga-jigan jam’iyar APC ranar alhamis 14 ga watan Satumba ciki har da shugaban jam’iyar John Odigie- Oyiegun.

Bisa bayanin da kakakin jam’iyar Bolaji Abdullahi ya fitar ministan ta bada hakuri game da tsokacin da tayi.

“ Tunda maganar ya taso jam’iya APC bata ce komai ba domin ko wa yana da nashi ra’ayi kuma yan jam’iya nada damar bayyana ra’ayin shi”

Mun tattauna da ministan don mu ji abun da tace kuma musan dalilin da yasa ta yi haka kana mu san yadda zamu bata amsa. ta yi hakikanin bayanin akan batun.

Bayan bayanin da tayi mun  gane cewa a matsayin ta na yar jam’iya tana da damar furtar da ra’ayin ta kuma tana da ra’ayin zabin duk wadda take so.

Amma a matsayin ta na jigo cikin jam’iay bai kamata tayi irin tsokacin da tayi a dai dai lokacin da ta furtar dashi. Ministan kuma ta bada hakuri indai tsokacin tayi ya kawo ma jam’iyar matsala. Ta bada hakuri” kakakin yace yayin da ya gana da manema labarai bayan ganawar su da ministan.

A bayan Aisha Alhassan tayi sanar cewa zata goyi bayan Atiku Abubakar indai ya fito takara a zaben 2019.

Tsokacin da ministan tayi ya tayar da kura a ƙasar inda ma ana ta tunanin cewa za’a iya koran ta daga aiki game dashi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.