ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

A zamanin mulkin PDP a fadar shugaban kasa ake rubuta huƙuncin kotu - inji Lawan

Sanata Ahmed Lawan yace jam’iyar adawa na “cikin duhu” duk da huƙuncin da kotun koli ta fitar

Senate leader, Ahmed Lawan

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan yace mafi yawancin huƙunci da kotu ke ɗauka a rubuce yake a fadar shugaban kasa a zamanin mulkin jam’iyar adawa PDP

Ahmed Lawan ya sanar da haka a zaman da yan majalisar suka yi ranar laraba 11 ga watan Yuli lokacin da yake bada nashi ra’ayi dangane da huƙunci da kotun koli ta fitar dangane da rikicin shugabancin jam’iyar PDP

Jigon sanatoci ya zayyana cewa huƙunci da kotun koli ta fitar na nuna cewa mulkin shugaba Buhari ya yarda da raba iko ma ko wani ɓangare na tsarin mulkin demokradiyya.

“Yan nijeriya suka yi zaben don ganin jam’iyar PDP bata cigaba da mulki a kasa kuma jam’iyar zata cigaba da samun koma-baya” inji lawan.

ADVERTISEMENT

“Duk da haka muna ma ‘yan nijeriya murna dangane da huƙuncin da kotun koli ta dauka a mulkin jam’iyar APC. A zamanin mulkin jam’iyar PDP a fadar shugaban kasa ake rubuta huƙuncin kotu”

“Wannan na nuna cewa mulkin gwamnati mai ci ya yarda da raba iko ma ko wani bangaren tsarin mulkin demokradiyya kuma ya ba shari’a damar ɗaukar huƙunci da ya dace ma ko wani mai laifi”.

Wannan labarin ya fito bayan huƙunci da kotun koli ta fitar ranar laraba 12 ga watan Yuli inda ta kaddamar da Ahmed Makarfi a matsayin ainihin shugaban jam’iyar PDP.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT