ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Barawo ya jinjina ma jami’an tsaro bisa kama shi da suka yi (bidiyo)

Diallo da abokan aikin shi sun amsa laifin satar miliyan 50 kudin kasar Guinea (N2m) daga wani shago da ake siyar da wayoyi

Wani barawo a ƙasa Guinea ya jinjina ma jami’an tsaro da suka kama shi.

Barawon wanda bai taba tunanin cewa za’a kama shi ya sara ma jami’an yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai.

A cikin bidiyon dake ta yawo a yanar gizo mai laifin Boubacar Diallo wanda ke makarantar takanikal na garin Mamou dake ƙasar Guinea ya bayyana cewa ya san matsayin laifin da ya aikata kuma ya san cewa za’a iya gurfanar dashi a gidan yari.

Diallo da abokan aikin shi sun amsa laifin satar franc miliyan 50 kudin ƙasar Guinea (kimanin naira miliyan 2 kudin Nijeriya) daga wani shago da ake siyar da wayoyi

ADVERTISEMENT

Diallo yayi kira ga jama'a na a mara ma jami'an tsaro baya inda yace a cigaba da taimakon su wajen kawar da barna a al’umma.

Shi dai wannan barawon yayi nadamar laifuffuka da ya aikata kuma yace ba zai kara aikata su ba.

Ga bidiyon nan kasa;

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT