ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

"babu ko allurar sirinji a asibitin Aso Villa" cewar Uwargidan shugaban kasa

Aisha Buhari tace an kasa bata maganin wani dan rashin lafiya data yi a kwannan baya

Uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari tayi tir da halin tabarbarewa da asibitin fadar shugaban ƙasa ke ciki.

Aisha Buhari ta bayyana halin da asibitin ke inda tace ko allurar sirinji babu a asibitin a wani taro da aka gudanar a farfajiyar shugaban ƙasa ranar litinin 9 ga watan octoba.

Matar shugaban ƙasa tace an kasa bata maganin wani dan rashin lafiya data yi a kwannan baya.

"A ko wani shekara ana ware ma asibitin kudin kasafin ƙasa, kuma idan aka je asibitin za'a gan inda ake gyare-gyare duk da haka babu ko sirinji a asibitin. menene amfanin gyaran da suke indai har babu kayan aiki a cikin asibiti?" tace.

ADVERTISEMENT

A baya ita ma diyar shugaban ƙasa Zahra tayi tsokaci game da halin da asibitin ke ciki inda ta nuna rashin jin dadi game da abubuwan dake faruwa a asibitin.

Jim kadan bayan tsokacin da Zahra tayi, sakatare na dindindin na fadar shugaban ƙasa Jalal Arabi ya sanar cewa za'a fara amsar kudin daga mara lafiya a asibitin domin aiwatar da wasu ayyuka dake bukatan kudi.

Yace yin haka zai taimaka ma ma'aikatan asibitin da su gudanar da sauran ayyukan su ba tare da sai sun jira kasafin kudi daga gwamnati.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT