ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Abubuwa 7 da ya kamata ka sani game da sabon kakakin yakin neman zaben shugaba Buhari

Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon kakakin yakin neman zabe da shugaba Buhari ya nada

Ranar talata 17 ga watan Afrilu sanarwa ya fito na  nadin Festus Keyamo a matsayin sabon kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na zaben 2019.

Babban lauyan ya sanar da haka a shafin sa na kafar sada zumunta na twitter ranar talata 17 ga wata.

Ga wasu abubuwa da ya kamata a sabni game da shi:

1. Festus Keyamo haifaffen dan jihar Delta ne wanda aka haifa cikin shekara 1970.

ADVERTISEMENT

2. Ya kammalla karatun sa a jami'ar Ambrose Ali dake jihar Edo inda ya karanta ilimin shari'a.

3. Ya shiga cibiyar kungiyar lauyoyi cikin shekara 1993 kuma ya fara aikin alkalanci gadan-gadan duk a cikin shekarar karkashin zauren Gani Fawehinmi Chambers.

4. Yana da matsayin SAN kuma dan gwagwarmayar yakin neman  yancin dan adam ne kuma ya sha jagoranta shirye-shiryen kwato hakkin wadanda aka cutar kuma yana daya daga cikin manyan lauyoyi dake sukar harkar shugaban ci da shugabanni.

5. Shine wakilin Mujahid Asari Dokubo a kotu yayin da aka shigar da karar shi kotu kan laifin kisa. Haka zalika shine wakilin shugaban kungiyar MASSOB yayin da aka shigar da karar sa kotu kan laifin cin amanar kasa.

6. A cikin 2008 ya kai karar gwamnatin tarayya kotu kan zargi nada jami'ai masu hannu da shuni ta barauniyar hanya.

ADVERTISEMENT

7. Ya samu lambobin yabo da dama na cikin gida har ma da kasashen waje. A cikin shekarar 2017 wata kungiya dake kasar Amurka mai suna United States Global Leadership Council, ta karrama shi da lambar yabo na "Global human right Awards" bisa rawar da yake takawa wajen bin hakkin biladama da kuma faffufitikar da yake wajen tabbatar da adalci a tsarin shugabanci da shugabanni.

Hakika Festus Keyamo yana daga cikin manyan alkalai da ake ji dasu a kasar a halin yanzu bisa jajircewar shi wajen bin hakkin wadanda yake wakilta kuma yayi kaurin suna a kafafen sada zumunta bisa tsokaci da korafe-korafe da yake yi wajen tabbatar da kyakkyawar tsari daga gwamnati da masu jagorantar manyan kujerun mulki.

Sai dai wannan sabon nadin da shugaban kasa Muhammad Buhari yayi na bashi matsayin kakakin neman zaben sa ya janyo cecekuce tsakanin jama'ar kasa,

Yayin da wasu ke masa fatan alheri kan sabon matsayin da ya samu, wasu na ganin bai kamata a bashi wannan matsayin domin ba hurumin shi bane.

An fiye ba matsayin kakaki ko mai magana da yawun wanda ke neman kujerar mulki ga kwararrun ma'aikatan kafafen watsa labarai wadanda suka yi kaurin suna kuma suka kawo sauyi da cigaba a fannin watsa labarai.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT