ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya zata saki sunayen wadanda suka wawushe kudin jama’a - inji ministan shari’a

Ministan yace za’a saki sunayen bayan gwamnati ta cika ka’idojin shari’a

Abubakar Malami

Gwamanatin tarayya tace zata saki sunayen barayin gwamnati wadanda suka wawushe kudin jama’a ma idon jama’a

Babban kotun tarayya dake jihar Lagos ta umurci gwamnatin Muhammadu Buhari da ta bayyanar da sunayen wadanda ake zargin  wawushe kudin jama’a.

Hakika gwamnatin tarayya tayi iƙirari cewa huƙumar yaki da rashawa (EFCC) ta gano wasu maƙodan kudi daga wasu barayin gwamnati amma ta ki bayanar da sunayen su.

Bayan umurnin da kotu ta bada, gwamnati ta yarda da wallafa sunayen wadanda ake ma zargin wawushe kudin jama’a idan  ta cika duk wani mataki/ka’ida da ya kamata ta bi na shari’a.

ADVERTISEMENT

A bayanin ministan shari’a Abubakar Malami, sai an bi matakai da shari’a ta yi  umurni.

Babban lauyan gwamnatin tarayya ya yi wannan bayani a fadar gwamnatin tarayya ranar laraba 5 ga watan Yuli.

Malami ya kara da cewa jiran tsammani daga hukuncin kotu yasa gwamnati baza ta iya bayanar da wasu labarai game da barayin gwamnati.

Mai shari’a Hadiza Shagari ta umurci gwamnatin tarayya da ta saki sunayen wadanda ake zargin wawushe kudin gwamnati ma idon yan kasar bayan karar neman  ‘yancin labari da huƙumar SERAP ta yi

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT