ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

mutum 3 sun mutu sakamakon wani sabon hari da aka kai garin Maisamari

Wannan lamarin ya faru ne bayan yan kwanaki da faruwar rikicin kabilanci a wasu sassa na jihar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 24.

Harin bazatan ya faru ne a yankin garin Maisamari dake nan karamar hukumar Sadauna na jihar. hukumar yan sanda na jihar ta tabbaar da harin ga jama'a.

kakakin rundunar yan sanda na jihar Taraba David Misal ya sanar cewa harin ya faru yayin da ake gudanar da wani bikin grgajiya mai suna Nding-Chin a nan garin Maisamari.

kamar yadda kakakin ya sanar, harin ya faru ne bayan yan sanda sun baiwa jama'a lokacin kammala bikin ganin yawan mutane da bikin zai jawo daga garuruwa daban daban.

Amma suka bijir ma lokacin da jamián suka kayyade masu inda har suka cigaba da bikin har cikin dare. wasu da dam suka koma gidan wani Yaya Ahmadun inda suka cigaba da bushashar bikin Ndong-Chin.

ADVERTISEMENT

"A dai dai lokacin da suka cigaba da bikin cikin dare ne wasu yan biniga suka kai masu hari har suka kashe mutum 3 tar da raunata mutum 6" cewar Godwin Sol mukaddashin shugaban karamar hukumar Sardauna.

Sol ya kara da cewa an kama wadanda suka hada bikin tare da shugabannin kabilar.

Shugaban ya sanar cewa wadandfa suka jikata suna amsar kulawa a babban asibiti dake nan  Gembu.

Babban abun bakin ciki da ya baiwa mukaddashin shugaban karamar hukumar haushi shine ganin yadda aka gudanar da taron gargajiya bayan gwamnati ta kafa doka dake yin hani domin samun mafita wajen inganta harkar tsaro a jihar bisa ga yawan rikici dake barke wa tsakanin kabilun jihar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT