ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tambuwal ya naɗa ɗan Dasuki a matsayin shugaban ƙamfanin zuba jari

Gwamnan ya umurci shi da ya sadaukar da kansa domin ɗaukan alhakin dake tare da mukamin kuma yayi amfani da ƙwarewarsa wajen bunkasa harkan kasuwanci a jihar

Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Tambuwal ya nada Malam Muhammadu Buhari Dasuki a matsayin shugaban ƙamfanin zuba jari na jihar (Sokoto investment company Ltd).

A wata takarda da kakakin sa Bashir Imam Imam ya fitar ranar talata 12 ga watan Satumba 2017 gwamnan ya ce sabon shugaban ƙamfanin Sokoto investment company zai shigo ne da ƙwarewarsa don bunkasa ƙamfanin.

Gwamnan ya umurci shi da ya sadaukar da kansa domin daukan alhakin dake tare da mukamin kuma yayi amfani da ƙwarewarsa wajen bunkasa harkan kasuwanci a jihar.

Dan ɗan marigayi sultan na sokoto Alhaji Ibrahim Dasuki zai maye gurbin tsohon shugaban ƙamfanin  marigayi Aliyu Bala Sokoto wanda ya rasu ranar 19 na watan Yuli.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT