ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hadarin jirgin kasa yayi sanadiyar mutuwar mutum 3

Lamarin ya faru safiyar ranar alhamis a garin Agege dake nan jihar Legas

Mutum uku sun mutu sanadiyar hadarin da ya faru yayin da jirgin kasa ya kauce daga hanyar tafiyar ta a yankin Abatoir nan karamar hukumar Agege na jihar Legas ranar safiyar ranar alhamis.

A labarin da jaridar guardian ta fitar, kakakin hukumar yan sanda na jihar Olarinde Famous-cole yace jirgin yaci karo da babban mota dake dakon kaya wanda ya sanya mutane da dama sun ji rauni har mutum 3 suka mutu.

"mun samu labarin abun da ya faru, mun tura jami'an mu dake kusa da wurin kuma nan ba da jimawa ba zamu sanar maku da cikakken bayani kan lamarin."kakakin ya shaida wa manema labarai.

Su hukumar bada agaji na gaggawa ta jihar (LASEMA) ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT