ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kama mutum 3 bisa ga laifin mallakar bingidar AK 47 da kunshin albarusai

Sale yace masu laifin sun hada hannun wajen siyan bindigar AK 47 tare da kunshin albarusai 30 daga hannun wani mai suna Kuru a kan N500,000

Kotun majistare dake unguwar Rijiyar Zaki nan garin Kano ta gurfanar da wasu mutane uku zuwa gidan yari bisa ga laifin mallakar bindigar AK 47 ta hanyar da ta sabawa doka.

Masu laifin Aliyu Yunusa da Alti Sani da Musa Umar wanda asali yan jihar Zamfara ne za’a tuhume su bisa ga aikata laifufuka da ya shafi sata.

Malam Aminu Fagge na kotun ya bada umarni na a cigaba da rikon su a gidan yari har sai ranar da zasu kara zuwa kotun domin jin hukunci da kotu zata zartar.

Dan sandan da ya gurfanar dasu gaban kotu sufeto Yusuf Sale ya fada ma kotun cewa sun aikata laifin cikin 2016.

ADVERTISEMENT

Sale yace masu laifin sun hada hannun wajen siyan bindigar AK 47 tare da kunshin albarusai 30 daga hannun wani mai suna Kuru (wanda suke nema ruwa a jallo) a kan N500,000.

A bisa bayanin shi masu laifin sun bada hayar bindigar ga wani Wada Mohammed dake karamar hukumar Doguwa na jihar Kano cikin watan Janairu na bana inda shi Mohammed yayi amfani da bindigar wajen yin garkuwa da mutane a jihar Kano da Kaduna.

Laifin su ya sabawa wa kundin tsarin dokar ƙasa.

An kara ranar jin kara zuwa 23 ga watan octoba na bana.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT