ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jami’an hukumar yan sanda sunyi zanga-zanga na rashin biyan albashin su

Sama da jami’ai 2000 suka taru a ofishin biyan albashi nan hedkwatar yan sanda na jihar domin nuna rashin jin dadin su

Sama da jami’an 2000 na hukumar yan sanda na jihar Kaduna suka kai koken su titin garin Kaduna na rashin biyan albashin watan Augusta da Satumba ranar litinin.

A bisa rahoton premium times, jami;an masu zanga-zanga sun taru a ofishin biyan albashi na rundunar yan sanda dake nan hedkwatar inda suke bukatar a biya albashin su.

Wasu daga cikin jami’an sun daura ma ministan kudi Kemi Adeosun laifin rashin biyan albashi domin bata bayyana ma shugaba Mahammadu Buhari hakikanin gaskiya game da yadda hukumar take.

Daya daga cikin su yana cewa “ tayi ma shugaban kasa karya cewa komai daidai yake a ko ina. Ta yaya za’a yaki cin hanci da rashawa indai ba’a biyan yan sanda albashin wata biyu.

ADVERTISEMENT

Kwamishnan yan sanda na jihar Cyril Abeh ya sanar cewa jinkirin ba laifin hukumar bane face laifin ma’aikatar kudi.

Banda jihar Kaduna, sauran jihohi da ake bin jami’an albashin watan  Agusta da Satumba sun hada da Kebbi Gombe, Nasarawa, Ekiti ,Bayelsa, Imo da Ogun.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT