ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mutum 6 sun rasu, 5 sun samu rauni a harinda aka kai karamar hukumar Bassa

Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda Terna Tyotev ya fada ma manema labarai a garin Jos cewa maharan sun kara da kona gidaje 10

Hukumar yan sanda na jihar Filato ta tabbatar da rasuwar mutum 6 tare da jikata mutum 5 a harin da aka kai kauyen Taagbe dake karamar hukumar Bassa a daren ranar asabar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda Terna Tyotev ya fada ma manema labarai a garin Jos cewa maharan sun kara da kona gidaje 10.

Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikata asibiti domin neman magani.

Wannan harin ya faru bayan kwana daya da gwamnan jihar Simon Lalung ya kafa dokar hana fita a karamar hukumar domin kawo karshen hare-hare da ake kaiwa al'ummar yankin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT