ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kama jami'in yan sanda da ya kashe manoma 7

A rahoton da NAN ta fitar an kama jami'in ne bayan takaddamar da wata kungiyar farar hula mai suna Progressive Mind for Development Initiate ta rattaba hannu a ciki.

A takardar wanda shugaban kungiyar Abubakar Abdulsalam ya sanya hannu a ciki, an zargi jami'in da aikata laifin cikin ranar 23 na watan Nuwamba 2017.

Takardar ta nuna  cewa jami'in dan sanda yayin da yake jagorantar tawagar sa masu safarar a kan babban titi sun kama manoman yayin da suke aiki a gonar su dake garin Gombi bayan haka sai suka daure su kana suka harbe su har suka mutu.

Duk a cikin takardar ana kara zargin jami'in da kashe wasu mutane 4 wanda aka zargi da yin sata lokacin da yake kula da wata ofishin yan sanda dake kauyen Kem na karamar hukumar Shelleng nan jihar Adamawa ranar 30 ga watan Afrilu na 2016.

ADVERTISEMENT

Kungiyar ta nuna facin ran ta game da laifin inda take shelar cewa idan har jami'an da ya kamata su tabbatar da tsaro suna aikata hakan, toh lalle idan har ba'a dau matakin kan lamarin za'a cigaba da samun ire-iren laifuffukar daga jami'an tsaro.

Kakakin yan sanda na jihar Othman Abubakar ya tabbatar da kama jami'in inda ya kara da cewa an gurfanar dashi har zuwa bayan kammala bincike a kan shi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT