ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

“Akwai dangantaka tsakanin boko haram da wasu ƙungiyoyin yan ta’ada dake Mali” - inji shugaban hafsan sojoji

Buratai yace an gano haka lokacin da aka cafke wasu kurtun kungiyar Boko haram Senegal da Mali.

Chief of Army Staff, Maj. General Tukur Buratai

Babban hafsan sojoji janar Tukur Buratai ya bayyana cewa kungiyar boko haram na da alaka da wasu kungiyoyin yan ta’adda dake arewacin kasar Mali.

Bisa ga labarin da jaridar Punch ta fitar, Buratai yayi wannan bayanin ranar litinin 10 ga watan Yuli yayin da ya je tarban shugaban hafsan sojoji na kasar Mali Babi Abdulrahman.

Buratai yace an gano alakar yayin da a kama wasu masu kurtu na ƙungiyar a kasar Mali da Senegal.

Ya ce, “ kasar nijeriya da Mali na fuskantar kalubale iri guda a kan ta’addanci. Yanda lamarin su ke neman yaduwa zuwa ko ina ya kamata mu hada gwiwa don kawo karshen ta’addancin.”

ADVERTISEMENT

“An gano cewa ƙungiyar Boko haram dake nijeriya na da alaka da wani ƙungiyar ta’addanci dake arewacin kasar Mali.”

“ an tabbatar da haka yayin da aka kama wasu kurtu na ƙungiyar a kasar Mali da Senegal. A shirye muke mu hada gwiwa da ku don yakar ta’addanci.”

“Duk wata barazana da arewacin Mali ke fuskanta kwatankwacin shi na faruwa a nan nijeriya don akwai dangantaka tsakanin yan boko haram da yan ta’adda dake Mali.”

Buratai ya nanata cewa sojoji sun durkusar da lamuran yan boko haram a arewa maso gabas duk da cewa kwanan baya yan ƙungiyar sun kai hare-hare a yankin.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT