ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mukaddashin shugaban kasa ya gana da Shugaba Buhari a birnin London inda yake jinya

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo wanda ke maye gurbin sa tun 7 ga watan mayu.

Professor Yemi Osinbajo and President Muhammadu Buhari

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin London ranar talata 11 ga watan Yuli 2017.

Ganawar wanda shine na farko da zasu yi tunda Shugaban yaje yin jinya ya faru a fadar Abuja house dake birnin London.

Ba’a samu hotuna yayin ganawar amma Sahara Reporters sun sako bidiyo wanda ke nuna mukaddashin yayin da yake barin Abuja house inda suka tattauna da shugaban.

A daren talata ne mai magana da yawun mukaddashin Laolu Akande ya wallafa a shafin sa na twitter cewa mukaddashin zai gana da shugaban kasa kuma zai dawo kasar nan da nan bayan sun gama tattaunawan.

ADVERTISEMENT

A safiyar yau kuma ya sanar cewa mukaddashin ya dawo birnin tarayya, ya wallafa cewa “ mukaddashin shugaban kasa ya dawo Abuja daga birnin London kuma zai jagoranci taron ministoci da za’a yi karfe 11 na safe a fadar shugaban kasa”.

Ya kara da wallafa cewa ya dau alkawarin sanar ma ‘yan nijeriya sakamakon tattaunawan da mukaddashin ya yi da shugaban, “nan ba da jimawa zamu sanar maku sakamakon ganawar da mukaddashin ya yi da shugaban, kyakywar tattaunawa ne, Allah ya albarkaci kasar mu nijeriya”.

Kusan kwana 66 kenan da shugaba Buhari ya koma birnin London don yin jinyar rashin lafiya da yake fama da ita.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT