Gwamnatin jihar jigawa ta ƙaddamar da ranar juma’a 7 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu don ma’aikata su taimaka wajen yi wa shugaba addu’a na samun lafiya cikin gaggawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada hutun kwana daya don yi wa shugaba Buhari addu’a
Gwamnatin ta bada hutun don ma’aikata da sauran yan jihar su taimaka wajen yi wa shugaba Buhari addu’a ta mussamman na samun lafiya.
Jami’in hulda da jama’a na huƙumar ma’aikata na jihar Alhaji Isma'il Ibrahim ya sanar da haka a wata bayani da ya fitar ranar al’hamis a garin Dutse.
Ibrahim yace fadar gwamnatin ta yanke shawarar bada hutun bayan wata zama da tayi ranar 5 ga watan Yuli
Yace gwamantin ta ƙaddamar da ranar juma’a a matsayin ranar hutu don ma’aikata da sauran mutane jihar su taimaka wajen yi shugaba Buhari addu’a na sauki daga rashin lafiya da yake fama da ita.
“A wannan ranar na hutun ana sa ran cewa ma’aikatan da sauran al’ummar jihar zasu taimaka don yi wa shugaban mu addu’a na Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa” yace.
“Kuma muna fatan zasu yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule addu’a Allah yasa Aljanna ce makomarsa” ya kara.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng