ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Uwargidan shugaban kasa tace “ saura kiris a kori karnukan da kurayen”

Uwargidan ta isar da sako mai ma’ana a boye don mayar ma Sanata Shehu Sani martani dangane da sakon da ya fitar a shafin shi na Facebook.

First Lady, Aisha Buhari returning from London on June 6 after meeting with President Muhammadu Buhari

Aisha Buhari to isar da wani sako mai nuna alamun cewa Shugaba Muhammadu Buhari na gab da dawowa kasar lokacin da ta bada nata ra’ayin a wani sakon da aka fitar a kafar sadarwa na facebook.

Uwargidan shugaban kasa ta isar da wani sako mai ma’ana a boye don mayar ma sanata Shehu martani bisa ga labarin da ya fitar a shafin shi na facebook mai ma’ana a boye.

Sanata ya rubata “ ana ma sarkin daji zaki addu’ar samun lafiya; sai dai ya dawo da karfin shi mutane zasu taru a fadar shi don mika gaisuwa. A yanzu dai karnuka da kuraye na tsare-tsare cikin waswasi don suna shakka ko sarki zaki zai dawo ko ba zai dawo ba.”

“Yanzu sarki zaki na bacci kuma babu wanda ya san ko zai tashi. Kuraye na fatan kada sarki zaki ya tashi ko kuma kada ya dawo dajin don su cigaba da mulki. Sauran kananan dabbobi na addu’a na sarkin ya dawo don ya tsiratar da su daga hannun kuraye, karnuka da sauran miyagun dabbobi”

ADVERTISEMENT

Don mayar da martani, Aisha ta rubuta “Allah ya amsa addu’o’in kananan dabbobi masu rauni, ana gab da koran karnukan da kuraye daga masarautar. Mun yarda da addu’o’in da goyon bayan da kananan dabbobi suke bada wa, Allah ya taimaki kananan dabbobi, Allah ya taimaki nijeriya.”

Indai an tuna, Shugaba Muhammadu Buhari ya koma kasar Ingila ranar 7 ga watan Mayu don neman maganin ciwon da yake fama da ita.

Kuma ranar laraba 5 ga watan Yuli uwargidan ta koma kasar don jinyar Maigidan ta.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT