ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Uwargidan shugaban kasa ta koma London don ganin mijinta

A wata sanarwa da mai magana da yawunta Suleiman Haruna ya fitar tace “za ta isar wa shugaban kasar sakonnin alheri da al’ummar kasar ke aika masa”

First Lady, Aisha Buhari

Rahotanni sun nuna cewa zata tsaya a kasar habasha don halartar taron matan shugabanin kasashen afrika kan cutar kanjamau ranar litinin 3 ga watan Yuli.

Mai magana da yawun uwargidan, Suleiman Haruna yace zata isar da sakon alheri da yan nijeriya ke yi wa shugaban kasar.

Haruna yace, “ana sa ran zuwan ta kasar habasha don halartar taron matan shugabannin kasashen afrika kan cutar kanjamau ranar litinin 3 ga watan Yuli.”

ADVERTISEMENT

“Zata hadu da sauran yan kungiyar wajen bikin ranar tunawa na shakaru 15 na kungiyar kuma zata amfani da damar wajen yin jawabin hakkin yin zabe dangane da zaben kasar nijeriya dake masowa.

“Zata cigaba da tafiyar ta zuwa kasar britaniya don ganin mijinta ranar talata 4 ga watan Yuli 2017.”

A baya dai gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose yace uwargidan shugaban kasa bata samu damar ganin mijinta tafiyar ta ta farko zuwa london.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT