ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wasu yan bindiga sunyi garkuwa da mai kula da harkar kasuwanci na hukumar NHIS

Ma’aikacin na hanyar tafiya daga Abuja zuwa Kaduna yayin da yan bindigar suka tare shi a babbar hanya dake kusa da garin Katari.

Kidnap

An samu labari cewa wasu yan bindiga sunyi garkuwa da mai kula da harkar kasuwanci na hukumar inshorar kiwon lafiya NHIS Zakari Muhammed Sada.

Rahoto ya bayyana  cewa Sada na hanyar tafiya zuwa kaduna daga Abuja lokacin da yan bindigar suka tare motar shi a babban hanya kusa da garin Katari.

Yan tawayen sun shiga daji da shi inda suka nemi iyalin shi da su biya kudin fansar shi.

Ba’a samu labarin yawan kudin da yan garkuwan suka bukaji iyalin sa su biya lokacin da aka yi wannan rahoto.

ADVERTISEMENT

Rundunar yan sanda na jihar basu samu sun tabbatar da lamarin lokacin da ake tunanin ya faru.

Wannan lamarin ya faru bayan wasu yan bindiga da ake tunanin yan garkuwa da mutum ne suka kai hari ma matafiya ranar juma’a 7 ga watan Yuli a babban hanya sashen garin Katari inda ma suka kashe wata mace.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT